Rundunar yan sandan jahar Kano, ta cafke wasu yan Dabar siyasar 54, dauke da muggan makamai da kwayoyi a ranar Idin Sallah, bisa zarginsu da yunkurin hana gudanar da bikin hawan Daushe a ranar Alhamis 11 ga watan Afrilun 2024.
Mai Magana da yawun rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai a wannan rana ta Alhamis.
SP Kiyawa, ya ce daman hukumomin tsaron jahar suna sane da yadda wasu ke shirin tayar da hankulan al’umma, inda ya ce akwai isassun jami’an tsaro da na’urorin da za su dinga ba su bayanan yadda abubuwa suke kasancewa a wurare daban-daban.