Wata Kotun tarayya ta jingina dakatar da GANDUJE daga jam'iyyar APC
Author -
Bashir A Bashir
April 18, 2024
0
Babbar kotun tarayya ta jingine hukuncin da kotun jihar kano tayi na dakatar da Dr Abdullahi Umar Ganduje shugaban jam'iyyar APC na kasa daga mukaminsa.
Hakan na zuwa ne bayan da wasu daga cikin shugabannin jam'iyyar sa ta APC a matakin mazaɓa suka sanar da dakatar dashi daga jam'iyyar.
Kotun ta kuma ce zata cigaba da sauraron shari'ar nan gaba kadan idan ta gama nazari a kan shari'ar.