Cibiyar wayar da kai da samar da kyakkyawan shugabanci ta Afrika wato (Africa Centre For Leadership, Strategy & Development) ta gabatar da taron wayar da kai kan cin zarafin ƴaƴa mata, taron wanda ya samu halartar dukkanin Sarakunan gargajiya na jihar Kano da Sarakunan Yarukan dake zaman su a jihar Kano wanda suka haɗar da Sarkin inyamurai, Sarkin Yarabawa da sauransu ciki har da ma wakilan gwamnatin jihar wanda suka samu wakilcin shugabar hukumar kula da al'amuran mata, yara da masu buƙata ta musamman.
Shugabar cibiyar ta Africa Centre For Leadership Strategy & Development (Dr. Margaret Fagboyo) tace wannan cibiya na iya ƙoƙarin ta ganin sun wayar da kan al'umma kan kyakkyawan tsarin zamantakewa tsakanin al'umma tare da wayar da kansu don ganin sun dakile yawaitar aukuwar cin zarafin ƴaƴa mata wanda hakan ya zama ruwan dare a musamman jihohin Kano da Benue wanda wannan jihohi sun fi kowace jiha samun yawaitar aukuwar wannan lamari na cin zarafin ƴaƴa mata.
Haj. Sa'adatu Sa'id wadda ke zama Permanent Secretary ta hukumar kula da al'amuran mata, yara da masu buƙata ta musamman tayi nata jawabin inda ta bayyana cewa: hukumar su ta shirya tsaf domin aiki da wannnan cibiya hannu bibbiyu da kuma bata duk wata dama da suke buƙata daga gare su.
A ƙarshe shugabar kungiyar lauyoyi mata ta Najeriya ta ƙara da cewa: a koda yaushe cikin bibiyar ƙorafe-ƙorafen cin zarafin mata da yara suke amma haƙan su baya cimma ruwa kasancewar babu kyakkyawan tsari daga gwamnati na tabbatar da hukunci cikin ƙanƙanin lokaci wanda hakan ke baiwa masu ƙorafi a gaban kotu dama su kansu masu bibiyar irin wannan ƙorafe-ƙorafen ke shan wahala wanda hakan ke sa wasu iyayen ke haƙura da kaiwa ƙara kotu yayin da irin wannan cin zarafi ya afka musu.