A zaman kotun na yau laraba, lauyan bangaran masu kara Barista Tanimu ya bayyana wa kotun cewa wacce ake zargin, ta jima tana gujewa shari’a, duk da sammacin da kotun ta yi umarnin a bai wa Sadiya Dauda Ican-Kabarin domin ta bayyana a gaban kotun.
Barista Tanimu ya sheda wa kotun cewa, wacce ake zargin ta yi wani fefan bidiyo tare da bata sunan mahaifin mai kara Adamu Abdullahi Karkasara wanda kuma ta yada bidiyo a kafafan sada zumunta.
An rawaito cewa lauyan masu karar ya sake nantawa kotun cewa, mako guda ana neman Sadiya Ican-Kabari domin a bata sammacin amma kuma har kawo yanzu sun gaza samun ta, sakamakon yadda ta kashe wayoyin da ta ke amfani da su.
Daga bisani mai shari’a Malam Abdu Abdullahi Wayya, ya amince da rokon bangaran ma su kara, tare da yin umarnin, a sake aikewa Sadiya Dauda Ican Kabari sabon sammacin ta hanyar like mata a kofar gidan ta da sakon kartakwana da kuma hanyar WhtaApp domin ta bayyana a kotun.
Alkalin kotun ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 5 ga watan gobe domin ci gaba da sauraron shari’ar kamar yadda jaridar idongari.ng, ta ruwaito.