Abba Gida Gida ya ceto rayuwar 'yar Sarki Ado Bayero daga tozarcin Gidan haya
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amsa roƙon diyar Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, mai suna Zainab Jummai Ado Bayero, bisa wa'adi da aka bata na inda take zaman haya a jihar Lagos tare da Mahaifiyarta da kuma dan uwanta, akan su tashi ko kuma a tashe su.
Babban Daraktan yaɗa labaran gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, wanda yaje jihar Lagos a wannan rana domin magance matsalar da Zainab ke fuskanta, yace tabbas ya lura da cewa, Zainab da Mahaifiyarta tare da dan uwanta, na cikin yanayi mara dadi tun bayan rasuwar mai martaba sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.
A baya bayan ne dai Zainab ta nemi agaji daga gwamnatin jihar Kano da kuma sarkin Kano Khalifa Muhammad Sanusi II, dukda tace tayi kokarin rufe halin da suke ciki saboda kasancewarta yar Gidan Sarauta, amma tace abin yafi karfinta inda ta nemi alfarma wurin Gwamna Alex Otti na Abia, da wasu makusanta mahaifinta, sai dai basu yi wani abu akan lamarin ba.