Gwamna Ahmed na Sokoto ya samu amincewar majalisar zartaswar jihar domin mika wani kudiri ga majalisar dokokin jihar da ke neman yin gyara ga dokar da ake da ita na nadi da tsige sarakunan gargajiya a jihar Sokoto. Za a gabatar da kudrin don yin tambari a ranar Litinin
Mafi yawa, kudirin na neman a kwacewa sarkin musulmi gaba daya ikon nadawa, dakatarwa, hukuntashi, mika mulki da dai sauransu, duk wani basaraken gargajiya har zuwa mai unguwa.
Iko É—aya zai kasance waje É—aya, kuma ya kasance ga gwamna gabaÉ—aya ba tare da tuntubar kowa ba.