Mai shari’a Yusuf Ubale Muhammad ya bayar da wannan umarni ne na wucin gadi a ranar 5 ga watan Yuni, 2024.
“An ba da umarnin wucin gadine ga wanda ake kara da kada ya sake ko shi ko wakilansa, abokan hulda, ko duk wanda ke yin aiki a madadinsa, daga kamawa, tsarewa, tsangwama, tsoratarwa, ko gayyatar, mai kara har sai an saurari karar da masu kara suka shigar.
“Ya kuma ba da umarnin cewa duka umarnin wucin gadi da aka bayar, a tabbatar a baiwa wadanda ake kara kafin ranar da aka sanya don sauraron karar,” in ji alkalin.