” Mun fito da sabbin dabarun ne ta hanyar cusawa ‘ya’yan mu kyamar cin hanci da rashawa, saboda idan yara suka taso da kyamar cin hanci to babu shakka akwai kyakykyawan yakinin za a kawar da shi, tun da an yake shi tun daga tushe”.
Babban Daraktan Cibiyar Farfesa Habu Muhammed Fagge ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai, Wanda aka shirya domin sanar da al’umma aiyukan da Cibiyar take gudanar ta fuskar yaki da cin hanci da rashawa a tsahon shekaru 6 da suka gabata.
Ya ce yadda cin hanci ya zama ruwan dare a cikin al’umma ya Zama wajibi a fito da sabbin dabaru domin yakar sa, saboda suma masu cin hanci suna fito da nasu dabarun a koda yaushe.
” Cikin wadannan shekaru 6 mun gana da rukunoni daban-daban na al’umma wadanda suka hadar da Malamai da Limamai da Fasto-fasto dake cikin al’umma, kuma sun ba mu kyakykyawan hadin kai, wanda hakan ya taimaka wajen samun nasarar wannan shirin”. A cewar Farfesa Habu Muhammed Fagge
” Haka zalika, Mun sami hadin kan kungiyoyi sama da 500 a fadin Nigeria, su ma kuma sun ba da tasu gudunnawar wajen samun wannan nasarar da muke alfahari da ita”. Inji Farfesa Habu Fagge
Ya ce a kokarin su na ganin sun wayar da kan jama’a illar cin hanci da rashawa sun ziyarci wurare daban-daban a cikin al’umma, wadanda suka hadar da makarantu da ma’aikatun gwamnati domin nan ne idan an Sami cin hanci zai fi cutar da al’umma fiye da ko’ina.
” Mun samar da litattafai da suke dauke da illolin cin hanci da rashawa, inda muka rabawa al’umma don su fahimci yadda cin hancin yake, saboda mun fahimci wasu basu ma san menene cin hancin ba Kuma zaka ga suna aikatawa ba tare da jin komai ba”. Inji Farfesa Habu Muhammed Fagge
Farfesa Habu Muhammed Fagge ya karawa da cewa babbar nasarar da suka samu ita ce shirin ya sami karbuwa sosai a cikin al’umma, musamman a jihohin Kano, Kaduna, Katsina da Lagos.
Ya ce wannan nasarar da suka samu ta basu kwarin gwiwa sosai ta ci gaba da sake zage damtse don wayar da kan al’umma irin illolin da cin hanci da rashawa ke da shi a cikin al’umma.
Da yake tsokaci kan aiyukan ta Cibiyar mumbayya na wayar da kan al’umma illolin cin hanci da rashawa, Farfesa Isma’il M Zango ya yaba da yadda cibiyar ta ke gudanar da aiyukan na ta.
Ya kuma yabawa babban Daraktan Cibiyar Farfesa Habu Muhammed Fagge da sauran wadanda suke taimaka masa wajen gudanar da aikin, bisa namijin kokarin da suke na yakar cin hanci da rashawa tun daga tushe.
Wannan shirin dai da Cibiyar Mambayya House ke gudanarwa a jihohin Nigeria, Gidauniyar MacArthur ce ke daukar nauyin sa .