Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a wata sanar da ta fitar yau, wadda ta samu sa hannun shugaban ƙungiyar, Aminu Ahmed Garko.
Sanarwa ta ce ta ɗauki matakin ne sanadiyyar cin zarafin da jami'an gwamnatin jihar ta Kano ke yi wa wakilanta a lokacin da suke gudanar da ayyukansu.
Sanarwar ta ce "duk wani yunƙuri da aka yi na tattaunawa da gwamnati da jami'anta domin warware matsalolin abin ya ci tura".
Sanarwar ta ci gaba da cewa wakilan kafafen yaɗa labarun sun ci gaba da fuskantar "hantara da tsangwama har ma da duka a lokacin da suke gudanar da ayyukansu".
Daga nan sai sanarwar ta ce ƴan jaridar ba za su sake ɗaukan rahoton duk wani taron manema labaru, ko ayyukan gwamnati ko tattaunawa da jami'an gwamnatin ba har sai gwamnatin jihar ta ɗauki alƙawarin kare ƴanci da lafiyar ƴan jarida.
Najeriya na daga cikin ƙasashen da ake wa kallon masu rauni wajen kare hakkin ƴan jarida.
A cikin rahotonta na shekara ta 2023, ƙungiyar kare hakkin ƴan jarida ta Reporters Without Borders ta ce ƴan siyasa a ƙasashe irin Najeriya na amfani da ƙarfinsu wajen daƙile ayyukan ƴan jarida, yayin da kuma wasu ƴan siyasar ke kafa nasu kafafen yaɗa labarun domin yaɗa farfaganda da labaran bogi.