Wasu kungiyoyi masu zaman kansu na arewacin najeriya sunyi kira ga gwamnatin tarayya kan ta saka idanu ta tabbatar cewa rikicin masarautu a jihar Kano bai yi sanadiyar rashin zaman lafiya da jihar ke taƙama dashi a faɗin arewacin najeriya ba. Kungiyoyin sun kuma yi kira ga shugaban kasar Najeriya Sanata Bola Ahmad Tinubu kan yasa baki kan rikincin tare da tabbatar da gaskiya a cikin shari'ar da ke gudana tsakanin Sarakunan biyu da ita kanta jihar Kano.
Sanarwar ta fita ne ta bakin shugaban wasu kungiyoyi masu zaman kansu a arewacin najeriya wanda ya nemi Æ´an jaridu da su sakaye sunansa, idan ya tattauna da manema labarai tare da jaddada aniyar su ta shiga cikin lamarin rikicin masarautun don tabbatar da an samu zaman lafiya a faÉ—in jihar Kano da kewaye baki É—aya.