Taron mai taken "Hujjoji a bayyane suke, mu zuba hannu jari don daƙile harkokin shaye-shaye" taron dai yayi daidai da ranar dakile harkokin shaye-shaye ta Duniya, ya kuma samu halartar manyan baƙi daga kowace hukumar tsaro dake jihar Kano.
Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa reshen jihar Kano Idris Abubakar ya bayyana irin ƙoƙarin da hukumar take don ganin ta daƙile harkokin Sha da fatauci na miyagun kwayoyi a jihar Kano inda yace suna iya ƙoƙarin wajen sa ido don ganin irin kayan basu shigo jihar ba kuma muddin suka shigo zasu ɗauki matakin kama su da kuma gurfanar da masu safarar gaban kuliya manta sabo don girbar abunda suka shuka, sanna da bibiyar guraren da suke samun rahoton sirri wanda ake gudanar da makamantan harkokin.
shugabar kungiyar fafutukar daƙile harkokin shaye-shaye wato (LESPADA) Amb. Maryam Hassan ta bayyana cewa kullum tunanin su shine ganin harkokin shaye-shaye sun zo ƙarshe a faɗin jihar Kano da Najeriya baki ɗayakuma kullum suna ƙoƙari don ganin sun samu haɗin gwiwar masu hannu da shuni domin hannu ɗays baya ɗaukar ninka.
Dr. Gwani Farouk Umar shugaban kungiyar (AREWA CONSULTATIVE FORUM) bayyana aniyar su ta ganin sun harhaɗa wasu adadin kuɗaɗe daga wajen ƴan kasuwanni don ganin sun tallafawa harkar daƙile shaye-shaye a jihar Kano da kewaye, tare da ginawa matasan da suka tuna makarantu don koyar dasu sabbin hanyoyin inganta rayuwa.
Cikin Hotuna: wasu daga cikin Kungiyar LESPADA da aka baiwa kyautar girmamawa bisa jajircewar don ganin an daƙile harkokin shaye-shaye a jihar Kano.