Taron mai taken "Ƙarshen Shirin ayyuka don kawo ƙarshen cin hanci da rashawa a Najeriya na tsahon shekaru shida tun daga shekarar 2018 zuwa 2024"
Shirin wanda Gidauniyar Mack Author ta ɗauki nauyi yayi duba da yadda cin hanci da rashawa yayi katutu a zukatan wasu daga cikin al'ummar Najeriya, inda Mumbayya House ta jagoranci gudanar da shirye-shirye na ganin ta kawo sauyi da kuma daƙile harkokin cin hanci da rashawa a Najeriya.
A ƙoƙarin Mumbayya House na ganin ta dakile harkokin cin hanci da rashawa tayi haɗin kai da kungiyoyi masu zaman kansu daga garuruwa daban-daban a faɗin Najeriya wanda suka haɗar da jihohin Gombe, Jigawa, Taraba, Maiduguri da sauran su, ciki har da kafafen yaɗa labarai.
Prof. Habu Muhammad Fagge shugaban Mumbayya House ya bayyana Gidan Mumbayya matsayin jigo wajen yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya inda sukai amfani da hanyoyi daban daban ciki har da koyar da wasu ƙananun kungiyoyi inda suka koyar dasu dabarun yaƙi da cin hanci da rashawa.
Shugaban shirin Prof. Isma'il Zango kuma tsohon shugaban gidan Mumbayya yayi ƙarin haske kan shirin tun daga fari inda yace suna alfahari da koyar da ɗalibai daga makarantu daban-daban a faɗin Najeriya don ganin sunyi watsi da ɗabi'ar cin hanci da rashawa tare da koya musu ɗabi'a mafi dacewa domin samun rayuwa mai inganci
Daga cikin kungiyoyin da suka gabatar da taƙaitacciyar muka sun haɗar da:
IMC, INAC, ICAN, UNNMC, MH.
Haka wasu wanda suka gabatar da taƙaitacciyar muƙala wanda suka kasance shugabannin kungiyoyin haɗin gwiwar sun haɗar da:
Cmr. Aqibu Garko da
Hashim H. Hashim daga Jigawa