Ba zan gudu ba ina gidan gwamnati ina jiran zuwan masu zanga-zanga domin karɓar Ƙorafe-Ƙorafen su ~ Gwamnan Kano.
Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ba zai gudu ko'ina ba yana gidan gwamnati yana jiran masu zanga-zangar lumana domin karɓar Ƙorafe-Ƙorafen su wanda mun rigada mun sani don kaiwa gaba. Gwamnan yayi wannan jawabi ne yayin da yake ganawa da manyan malaman addini da sauran masu hannu da shuni dake faɗin jihar Kano.
Manufar taron shine tattauna ƙananu da manyan matsaloli da jihar Kano ke ciki da nufin samo bakin zaren.