Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa Kwanakin bayan bayan ne gwamnatin jihar kano ta dawo da masarautar Rano a matsayin mai daraja ta biyu, bayan rushe dokar da ta samar da masarautun Rano, Gaya, Karaye da Bachi da tsohuwar gwamnatin Ganduje ta yi a Shekarar 2019.
Dan majalisar ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyon da ya karade dandalin sada zumunta, wanda kadaura24 ta kalla a yammacin ranar lahadi.
” Gaskiya ne masu cewa a dakatar da aiki Saboda ni ban goyi bayan rushe masarautu ba, to Gaskiya ne ni ban yarda da rushe masarautun mu ba, saboda mu Rano masu daraja ta daya ne haka Allah ya yi mu, idan ka ce ka dawo da mu masu daraja ta biyu to ka sani Ra’ayinsa ne, amma mu masu daraja ta biyu ne”. Inji Rurum
” Abun da aka yi mana na rushe mana masarautar mu ta Rano ba mu dadinsa ba, kuma ba ma goyon bayansa, mu a saninmu masarautarmu ta Rano mai daraja ta daya ce ba daraja ta biyu ba”.
Kabiru Alhassan Rurum ya ce ya yarda da duk abun da zai faru da shi, ya faru da shi, amma dai Matsayarsa ita ce bai Jin dadin abun da aka yi musu ba, kuma ya ce har yanzu su suna yiwa masarautar kallon mai daraja ta daya wacce ta ke da kananan hukumomi 10 a karkashinta.
” Ni mai neman zaman lafiya da kowa ne har yan adawa lafiya lau muke zaune da su, amma idan an kani bango lokaci zai zo da zan fito fadawa al’ummar mu abun da muka yi musu, kai ma sai ka zo ka fadi abun da kaima ka yi, hakan zai sa a gane wannene ni”. A cewar Kabiru Alhassan
Dan majalisar ya nuna cewa an dakatar da wani aiki a yankin karamar hukumar Rano sakamakon takun sakar da ake yi da shi, Inda ya ce wannan shi ne karon farko da ya yi magana akan abun dake faruwa.
Kabiru Alhassan Rurum wanda Dan majalisar tarayya ne a jam’iyyar NNPP ya ce “Lokacin Siyasa zai zo nan da shekaru biyu, Amma Matsayar mu ita ce ba ma goyon bayan rushe mana masarautar mu ta Rano”
Dama dai an jima ana hasashen akwai takun saka tsakanin Dan majalisar tarayya na kananan hukumomi Rano Kibiya da Bunkure da gwamnatin jihar kano ta Abba Kabir Yusuf.