Daily Nigeria ta ruwaito cewa Gargadin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da al’amura ke kara tabarbarewa a Kenya, inda zanga-zangar adawa da matakin da gwamnati ta dauka na kara haraji ta rikide zuwa neman ingantaccen shugabanci da kuma rajin cewa shugaba William Ruto ya yi murabus.
Sanata Lawan (APC/Yobe ta Arewa) ya bayyana hakan ne a yayin zaman majalisar a jiya Talata, yayin da ya ke bayar da gudunmawa ga kudirin da Sanata Karimi Sunday Steve (Kogi ta Yamma) ya mika tare da Sanata Mohammed Ali Ndume (Borno ta Kudu) kan “bukatar gaggawar a magance matsalar karancin abinci da kuma hauhawar farashin kayan masarufi a Najeriya.”
Ya bayyana matsananciyar yunwar da Æ´an Najeriya ke fuskanta tare da jaddada wajabcin majalisar dattawa ta gaggauta shigar da bangaren zartarwa kan lamarin.
Lawan ya ce, “Idan ba mu dauki matakin gaggawa kan karin farashin abinci da kudin wutar lantarki ba, ba za mu ji dadi ba irin abinda za mu gani a kan tituna ba. Ba za ta yiwu mu dau wannan lokacin muna wulakanta al’umma ba. ”