Shugaban hukumar, Farfesa Sani Lawal Malumfashi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da hukumar ta gudanar a babban dakin taro dake hukumar a safiyar wannan rana ta laraba.
Sani Lawal Malumfashi ya kara da cewar an kira taron ne domin sanar da jam'iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki sabuwar ranar zaben kananan hukumomin domin su kwana cikin shiri.
Ya kuma kara cewa an sanya sabuwar ranar zaben ne sakamakon hukuncin kotun kolin kasar nan da ta bada umarnin samar da mulkin kananan hukumomi bisa tsarin demokaradiyya.
Wakilin mu Musa Yahya Gyaranya ya ruwaito cewa shugaban hukumar zaben Farfesa Sani Lawal Malumfashi Ya bada tabbacin hukumar na gudanar da sahihi kuma karbabben zaben kananan hukumom, ya jaddada cewa basu lamunci duk wani yunkuri na muna rashin ɗa'a yayin yaƙin neman zaɓe da kuma lokacin zaɓe ba.