Ministan ya sanar da hakan ne yayin da yake yiwa manema labarai jawabi bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya a yau Litinin.
“Kuna sane da cewa Najeriya na tattaunawa da hadaddiyar daular larabawa kan batun bada biza ga ‘yan Najeriya dake son zuwa kasar.
” A yau an cimma yarjejeniya a kan hakan, daga yau 15 ga watan Yuli ‘yan Najeriya zasu iya samun bizar shiga kasar hadaddiyar daular Larabawa”, inji Ministan.