An yaye ɗaliban bayan shafe shekaru uku suna karatun NCE a kwalejin, ɗaliban wanda suka haɗar da mata 13 da maza biyu sun bayyana farin cikin su tare da yiwa Allah godiya daya nuna musu wannan rana mai ɗumbin tarihi a rayuwar su.
Shugaban kwalejin karatu ta Annur Mal. Auwalu Abubakar Sulaiman ya bayyana irin ƙoƙarin da kwalejin ke yi don ganin an yaye ɗalibai masu inganci musamman a kan harkokin koyarwa wato ɓangaren NCE ya kuma koka kan yadda daliban bangaren na NCE ke ƙara raguwa a duk faɗin Najeriya baki ɗaya.
Guda cikin ɗaliban da aka yaye (Zainab Sa'id Haruna) ta bayyana yadda karatun nasu ya canza musu rayuwa kasancewar sa'ar malamai masu koyar dasu da suka yi a yayin gabatar da karatun nasu a Kwalejin Karatun ta (Annur). Sannan tana alfahari da kasancewar ta cikin daliban da nan gaba kaɗan zasu iya fara koyarwa a ko'ina a faɗin Najeriya, ta kuma miƙa godiya ga iyayen ta da suka tsaya tsayin daka don ganin sun cika mata burin ta na kammala karatun data sa a gaba.
A ƙarshe Mal. Usman Mujittaba guda cikin malaman kwalejin kuma Shugaban Sashen tsare-tsaren karatu na kwalejin ya bayyana cewa kullum karatun NCE na ƙara zama koma baya wajen karantar da a Najeriya kasancewar ba'a baiwa harkar koyarwa muhimmanci a gwamnatance ba.
Cikin Hotuna: Yadda Aka gudanar da bikin yaye ɗaliban Kwalejin Karatu ta Annur, wato Annur College of Education Kano, da yadda malamai suka gudanar da muƙala..
1
3