Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arziƙi Ta’annati (EFCC) ta kasa gabatar da takardu a gaban Babbar Kotun Jihar Kano, wanda hakan ya kawo jinkiri a sauraron shari’ar tsakanin hukumar a da jagoran Jami’yyar NNPP na Kasa, Rabiu Musa Kwankwaso da wasu mutum bakwai.
Waɗanda aka shigar ƙarar sun haɗa da NNPP, Dokta Ajuji Ahmed, Dipo Olayanku, Ahmed Balewa, Cif Clement Anele, Lady Folshade Aliu, Injiniya Buba Galadima da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Lauya masu ƙara, Robert Hon, ya ce a shirye suke domin ci gaba da shari’ar.
Ya nuna cewa EFCC na da kwana biyar don shirya wa shari’ar, amma fiye da kwana 30 ta wuce ba tare da sun shirya ba.
Hon, ya bayyana cewa wannan shari’ar ta shafi ‘yancin ɗan adam ne, inda kuma ya roƙi kotu ta yi watsi da buƙatar EFCC na jinkirta shari’ar ba saboda ba su bayar da ƙwaƙƙwaran dalili.
Lauyan EFCC, Idris Ibrahim Haruna, ya nemi kotun ta ƙara musu lokaci domin su shirya amsarsu.
Alƙalin kotun, Mai shari’a Yusuf Ubale Muhammad, ya ɗage shari’ar zuwa ranar 24 ga watan Oktoba, 2024, domin ci gaba da sauraron ƙarar.
A baya kotun ta haramta wa EFCC kama ko tsoratar da waɗanda ake ƙara har sai an kammala shari’ar.