Masu garkuwa da mutane da suka sace mahaifiyar Dauda Kahutu Rarara sun bukaci a basu Naira miliyan 900 a matsayin kudin fansa.
Wata majiya mai tushe ta tabbatarwa da cewa, barayin sun tuntubi iyalan Rarara, inda suka tabbatar musu da cewa mahaifiyar tasu tana cikin koshin lafiya, kuma da zarar an biya kudin fansar zasu sake ta ba tare da É“ata lokaci ba.