Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta babbar kotun jihar Kano da ke zaune a sakatariyar Audu Bako, Kano, ta umurci lauyoyi a rikicin masarautu da su daina yin magana da manema labarai.
Alkalin kotun ta bayar da umarnin ne a lokacin da ake ci gaba da shari’ar, a ranar Alhamis.
Ta ce, “Umarni ne gare ku (lauyoyi) da kada ku sake yin wata hira da manema labarai kafin da kuma bayan yanke hukuncin kan dambarwar dake wanda ake kara na farko ya daukaka kara”.
Daily trust ta ruwaito cewa jim kadan bayan wannan umarni, alkalin kotun ta tafi hutu domin yanke hukunci kan takaddamar.
Idan dai za a iya tunawa, Babban Lauyan Jihar Kano, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano da Majalisar Dokokin Jihar Kano, ne suka shigar da karar ta bakin Lauyan su Ibrahim Isah-Wangida, Esq.
Sun shigar da karar ne a ranar 27 ga Mayu.
A karar suna neman kotu ta hana Aminu Ado Bayero da sarakunan Bichi da Rano da Gaya da kuma Karaye cigaba da ayyana kansu a matsayin Sarakuna .
Wadanda suka amsa sun hada da Alhaji Aminu Ado-Bayero da Alhaji Nasiru Ado-Bayero Bichi Sarkin Karaye da Dr Ibrahim Abubakar ll da Sarkin Rano Alhaji Kabiru Muhammad-Inuwa da Alhaji Aliyu Ibrahim-Gaya Sarkin Gaya.
Sauran wadanda ake kara sun hada da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Darakta Hukumar DSS, Jami’an Tsaron Civic defense da rundunar Sojojin Najeriya.