Sanatan Yana neman Majalisar dattawa ta Amince a Kirkiri Jihar Tiga.
Akwai yiwuwar samar da sabuwar jiha nan ba da jimawa, sakamakon yadda aka gabatar da kudirin kafa jihar Tiga daga Kano a majalisar dattawan Najeriya.
Kudirin doka mai taken “Constitution of the Federal Republic of Nigeria, 1999 (Alteration) Creation of Tiga State Bill, 2024 (SB.523)” na da nufin raba jihar Kano zuwa jihohi biyu, inda Tiga za ta zama sabuwar jihar da za a kirkireta daga jihar kano.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne Majalisar Dattawa ta karbi kudirin kafa Jihar Anioma a yankin Kudu maso Gabas, wanda Sanata Ned Nwoko daga Delta ta Arewa ya gabatar.
Bugu da kari, an gabatar da kudirin dokar kafa jihar Orlu, wanda Sanata Osita Izunaso da mai wakiltar Ikenga Ugochineyere, da kuma jihar Etiti suka gabatar, wanda dan majalisa Amobi Godwin Ogah da wasu ‘yan majalisa hudu daga al’ummomin da abin ya shafa suka dauki nauyinsa.
Akwai kuma kiraye-kirayen a kirkiro sabbin jihohi daga Legas da sauran sassan kasar nan.