Shugaban Kenya William Ruto ya kori kusan daukacin ministocinsa
Shugaban kasar Kenya William Ruto ya sanar da korar kusan daukacin ministocinsa sakamakon boren da gwamnatinsa ta fuskanta daga jama'a saboda tsadar rayuwa.
A jawabin da ya yi wa al'ummar kasar ta kafar talabijin, Ruto yace wadanda korar ba ta shafa ba sune mataimakin shugaban kasa Rigathi Gachagua da kuma ministan harkokin waje Musalia Mudavadi.
Akwai wani darasi da Nijeriya za ta iya dauka daga wannan garambawul?