Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Baffa Dan Agundi a matsayin sabon Darakta-Janar na Cibiyar kula da nagartar aiyuka ta Kasa (NPC).
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.
Dan Agundi tsohon shugaban masu rinjaye ne a majalisar dokokin jihar Kano. Ya kuma taba zaman babban magatakarda a babbar kotun shari’a ta jihar Kano.
Baffa Babba ya kuma taba zama Manajan Darakta na hukumar KAROTA ta jihar kano, sannan ya rike shugaban tawagar matasan yakin neman zaben shugaban kasa Bola Tinubu a arewa maso yammacin Nigeria.
Shugaban Kasar ya yi fatan sabon babban daraktan zai sanya kishin kasa wajen inganta aiyukan hukumar domin cigaban kasa.
“Ina fatan zaka yi amfani da gogewar da kake da ita wajen ciyar da wannan hukumar gaba.