Gwamnatin Najeriya ta ce ta rage farashin buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50 da kashi 50 zuwa N40,000 a fadin kasar.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a karshen taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka yi ranar Litinin a Abuja.
cewarsa, rage farashin shinkafar ya zo ne a daidai lokacin da aka tura motocin dakon kaya 20 ga gwamnonin jihohi daban-daban domin rabawa ‘yan Najeriya.
Ya ce sun kuma rage farashin Shinkafar da kusan kashi 50 na kudinta ga yan Nigeria, tuni an tura Shinkafar wurare daban-daban a jihohin kasar nan domin sayar da ita akan farashin naira dubu 40. An samar da cibiyoyi, ta yadda masu bukatar wannan shinkafa za su je can su saya a kan Naira 40,000,” inji shi.
A halin da ake ciki kuma, wani binciken da kadaura24 ta gudanar ya nuna cewa ana sayar da buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50 tsakanin N75,000 zuwa N80,000 a wasu daga cikin Kasuwannin Kasar.