Ministan ya ce matakin cire haraji kan wasu kayayyakin abinci ga gwamnatin shugaba Tinubu ta amince wa yan kasuwa shigo da su Najeriya da kuma ƙoƙarin gwamnati na shigo da tan dubu 500 na Alkama da Masara su ne manyan dalilan gwamnati na karya farashin a watan ɗaya na shekara mai zuwa, kuma ya ce gwamnati zata ƙaiyade farashi da za'a riƙa sayar da kayan na abinci.
Kyari ya ce sun samu kwarin gwiwar yin hakanne bayan shawara da ƙungiyar manoman Najeriya ta basu cewa yin hakan ne kadai zai sa a samu saukin rayuwa, saboda a cewar ƙungiyar manoman ta AFAN abinci da ake nomawa ba zai isa ba.
Wannan mataki na gwamnatin tarayya na zuwa shekara guda bayan cire tallafin man fetur, abin da wasu ke ganin kamar ya zo a makare, sannan ina ma ace a wannan lokaci na damuna za'a aiwatar ba wai har nan da kwanaki 180 ba.