al'amarin dai ya faru ne bayan da taje kantin ta kuma nemi a haɗa mata lefe ita da abokan sana'ar ta (Abubakar Hotoro da Mustapha).
Kantin sunce a baya ma ta taɓa musu makamancin wannan ta'asa inda ta tura musu nera miliyan 25 na bogi.
Bayan da aka gabatar dasu gaban kotu me lamba 70 dake zamanta a Nomansland ƙarƙashin Jagorancin Majistray Farouq Ibrahim Umar ne ya duba jaririn dake hannun ta wanda bai wuce kwana ashirin ba, zuwa ranar 12 ga watan Nuwamba, su kuwa abokan sana'arta za'a gabatar dasu a gaban Kotu ranar Alhamis 29 ga wannan wata da muke ciki.
Sai dai har izuwa yanzu ƴankasuwa daga bangarori da dama suna zuwa ofishin ƴansanda suna neman da abi musu haƙƙunan su saboda zargin cewa suma sun taɓa musu wannan ta'asa ta (Fake Alert).