Gwamnan Kano ne ya bayyana hakan cikin wani taro daya gudana a gidan Gwamnatin jihar tare da ƴanjaridu.
Wannan sanarwar dai ta faru ne duba da yadda wasu fusatattun matasa ke fakewa da zanga-zangar suna fasa shagunan wasu da ƙone-ƙone tare da ɗebe kayan jama'a.