"Lokaci bai ƙure ga shugabannin Arewacin Najeriya su farka ba su tsamo al'umma daga ƙuncin rayuwa" ~ Gwamna Uba Sani
Author -
Bashir A Bashir
August 03, 2024
0
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya ce lokaci bai ƙure ba ga shugabanni a arewacin Najeriya su farka, su tsamo al'ummominsu daga halin fatara da rashin ilimi da ke addabar yankin.
Gwamnan ya bayyana haka ne ga BBC a kan zanga-zangar da aka shiga a faɗin Najeriya.