Kungiyar SELF HELP AFRICA ce ta gabatar da wannan taro na tallafawa matasa a fannin noma tare da haɗin gwiwar gidauniyar MasterCard da WFP. Kungiyar
SELF HELP AFRICA ta bayyana matasa matsayin ƙashin bayan al'umma kuma ababen dogaro cikin al'ummar dake tare dasu, a don haka suka ga dacewar.
Shugabar sashen shirye-shirye
ta (Self Help Africa) Hajara Muhammad tayi ƙarin haske dangane da shirin inda tace zasu duba matasa musamman mata cikin kungiyoyin manoma na jiha dama ƙananun hukumomin Tudunwada da Kumbotso kamar yadda yake a jadawalin su tare da bibiya don ganin an a ɗora ƙwarya a gurbinta.
shugaban hukumar KNARDA Dr. Farouk Kurawa ya bayyana cewa tabbas kwalliya zata biya kuɗin sabulu duba da yadda aka zaɓo ƙananun hukumomi wanda aka shede su da aikin noma fiye da sauran harkokin rayuwar yau da kullum sannan wannan ƙari ne kan ayyukan tallafi da hukumar ta saba baiwa manoma ne ƙarƙashin Gwamnatin jihar Kano.
Shima shugaban ruƙo na ƙaramar hukumar Tudunwada Umar Isah Ahmadyace Kungiyar (Self Help Africa) da sauran takwarorinta sunyi kyakkyawan duba na shigo da ƙananun hukumomi irin nasu cikin shirin kuma musamman matasa da suka ambata tun da fari don inganta rayuwar su.