Gwamnatin Najeriyar ta yi Allah wadai da tashin hankalin da ake samu yayin zanga-zangar ƙuncin rayuwa da aka fara a sassan kasar a jiya Alhamis.
Malam Abdul'aziz Abdul'ziz, daya ne daga cikin masu magana da yawun shugaban Najeriyar ya sahida wa BBC cewa shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya san ƴan ƙasar na da ƴancin yin zanga-zangar tare da bayyana ra'ayinsu "amman abin takaici yadda aka fito a sassa daban-daban an ɓige da abubuwa waɗanda ba su bane yakamata agani a akan tituna."
"An ɓuge da cin zarafin marasa galihu da zubar da jini da kuma yin abubuwa na rashin ɗa'a da kuma rashin daidai, wannan abun gwamnati ta yi Allah-wadai da shi, ganin cewa mutanen da basu ji ba basu gani ba, an ƙuntata masu, anyi wa wasu asarar dukiyoyi, har wasu ma sun rasa rayukansu, har ma da jami'an tsaro." cewar Malam Abdul'aziz.
Gwamnatin Najeriyar ta ce ba ta san wadanda suka shirya zanga-zangar ba, wadanda ake iya cewa gasu kuma ba a Najeriyar suke zaune ba, shiyasa ba za ta iya tattaunawa da su ba.
"Babu wani wanda ya fito, in ba wadanda aka tsinta bisa titi ba, idan mutum bai fito ba ya yi abinda yake cewa shi yayi imani ya yi ba , ta ina zaka zauna dashi, mu bamu taɓa banzatar da koke-koken mutane ba," In ji Malam Abdul'aziz
Gwamnatin ta ce ta san halin da ƴan ƙasar ke ciki na matsin rayuwa, sai dai abu ne na ba yadda za a yi, "Ana ƙoƙari aga wane matakai yakamata a ɗauka domin a samu sauƙin wadannan abubuwa."
Masu zanga-zangar dai na neman gwamnatin Najeriyar ta dawo da tallafin man fetur da shugaban ƙasar ya sanar da janye shi a ranar da ya sha rantsuwar kama aiki, matakin da gwamnatin ta ce zai yi wahala a iya mayar da tallafin.
"A gwamnatance babu abunda za a ce ba za a iya yi ba, saboda mulkin jama'a ake, amman akwai abubuwan da suke kusan mawuyacin abu ne , yiyuwarsu ɗin akwai wahala, ba dan ba a san yi ba,sai dan dai misali kamar ka ce ka ɗebo ruwa ne daga ƙafaffiyar rijiyar da ba ta da ruwan, saboda babu kuɗin da za a iya amfani da su ayi wannan abun."
Malam Abdul'aziz ya ce idan mutane sun yi la'akari da abunda ya faru jiya ba lallai su sake fitowa ba " ai gani ya kori ji idan har mutane suka ga abunda suka faru jiya Alhamis a garuruwa daban-daban,kace kuma wai zaka sake yin zanga-zanga, to bana jin anyi aiki da hankali."