Shugaban kwamitin Justice Lawan Wada, mai ritaya ne ya bayyana hakan, a taron manema labarai da aka gudanar ayau Alhamis 5 ga watan Satumba 2024 a birnin Kano.
Zanga-zangar wadda aka gudanar a watan augustan 2024, inda rikide zuwa tarzoma, har aka yi asarar rayuka, dukiya da kuma kone-kone a wasu sassan birnin Kano.
A cewar kwamitin binciken da za su gudanar , shi ne zai tabbatar da hakan, tare da kiyasta kimar dukiyar da aka rasa.
‘’don haka za mu bi guraren da muna da niyar za mu bi wuraren da muka tabbatar an yi wadannan abubuwa za muje, mu gani da idon mu da kuma karbar abubuwan da suka rasa’’ cewar Justice L.Wada’’.
, gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ne ya umarci kwamitin da zai binciken kan tarzomar da aka yi lokacin zanga-zangar matsin rayuwa a jihar, da kada su sassautawa duk wanda aka samu da laifi.
Kwamitin ya ziyarci babbar kotun jahar Kano dake sakatariyar Audu Bako da kuma ma’aikatar Dab’I ta jahar Kano don ganin barnar da aka yi, a lokacin gudanar da zanga-zangar.
Haka zalika Justice L. W. Muhammed , ya kara da cewa suna fatan jama’a za su taimakawa kwamitin wajen kawo mu su labarin irin abubuwan da suka faru ba tare da jin tsoro ba.
‘’ idan al’umma ba su kawo mana labarin abinda ya faru ba babu abinda za mu iya yi’’cewar sa’’.
Ya kuma roki yan jarida da su fadakar da al’umma don suje su bayar da bayanai, ba tare jin tsoron komai ba, tunda dai doka ce ta kafa kwamitin kuma za su kare mutuncin kowa da hakkinsa.
Kwamitin ya kara da cewa a bangaren su za su yi adalci, bisa abubuwan da suka fahimta ba tare da fargaba ko shakkar kowa ba.
Ya kuma tabbatar wa da al’ummar jahar Kano cewa, babu wani jami’in gwamnati da zai tsoma mu su baki kamar yadda gwamnan jahar Abba Kabir Yusuf ya tabbatar mu su.
Kwaimitin dai yana saran karbar shawarwari daga malamai, sarakuna, Dattawa don daukar matakin dakile faruwar hakan anan gaba.
Idongari.ng, ta ruwato cewa kwamitin zai kammala aikinsa ne cikin watanni uku, don mika rahotansa kan abubuwan da suka faru.
Idan ba a manta ba wasu Bata-gari sun far wa ofishin Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) da ke Kano inda suka kwashe kwamfutoci da kujeru wasu kayan aiki masu tarzomar sun kuma cinna wuta a ofishin, da kuma shiga babbar kotun jahar Kano dake sakatariyar Audu Bako,kafin daga bisani jami’an tsaro su kawo dauki a wurin.
Haka zalika an farfasa manya da kananan shagunan siyar da kayan abinci, tare da yin awon gaba da su, sai dai suma jami’an tsaro sun yi nasarar kama wa da kuma dawo da wasu daga cikin kayan da aka sace.