Ɗan majalisar wakilai, mai wakiltar Ƙiru da Bebeji na jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa ya ce ba ɗari bisa ɗari yake goyon bayan ƙudurorin gyara haraji ba, sannan ya ƙara da cewa yana bayar da haƙuri.
BBC ta rawaito cewa Kofa ya bayyana haka a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yammacin ranar Laraba, inda a ciki ya ce, "babu wurin da ko sau ɗaya na ce ina goyon bayan sababbin dokokin haraji ɗari bisa ɗari."
A cewarsa, "Abin da na ce (shi ne) akwai batutuwa da dama waɗanda za su zama alheri ga yankin arewa da ma Najeriya. Kuma mu ƴan majalisa na yankin arewa mu yi amfani da rinjayen da muke da shi a majalisa mu yi tsayin-daka mu goyi bayan duk wasu ƙudurorin da za su amfani arewa ta fannonin bunƙasa tattalin arzikin yankinmu da suke cikin kudurorin. Sannan mu kuma cire waɗanda za su cutar da mu, ko mu gyara su ta yadda ba za su cutar da mu ba."
A cikin rubutun ya ƙara da cewa yana so ne yankin arewa su yi amfani damar dokar wajen bijiro da wasu sabbin hanyoyi, "mu shigar da su a cikin kundin ƙudirorin," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa, "ban taɓa ba, kuma ba zan taɓa goyon bayan duk wata doka ko ƙudirin da zai kawo illa ga mazaɓa ta, jihata ko Arewa da ma Najeriya ba."