An rufe filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke babban Birnin Tarayya Abuja bayan da wani jirgin sama ya gamu da fashewar taya lokacin sauka, inda ya kauce daga kan titin zuwa cikin ciyayi.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa yanzu haka jirgin ya makale a cikin ciyayi, lamarin da ya sanya dole aka rufe filin jirgin har sai an kammala janye shi daga wajen.