Majalisar Dattawa ta sake jaddada kudirinta na ci gaba da tafiyar da kudurorin gyaran haraji, inda ta bayyana cewa babu wani bangare na tsarin da aka dakatar ko aka janye.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana hakan a zaman majalisa ranar Alhamis cewa za a ci gaba da mayar da hankali kan wakiltar muradun 'yan Najeriya, kuma ba za a tsoratar da majalisar daga waje ba.
Bayan wani batu da aka tada ta hannun jagoran majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele, Akpabio ya musanta rahotannin kafafen yada labarai da ke cewa an dakatar da tattaunawa kan kudurorin ko an janye su.
Yayin da yake watsi da duk wani yunkuri na matsawa majalisar lamba, Shugaban Majalisar Dattawa ya kuma ce: “Ba za a tsoratar da majalisar dattawa ba. Duk wata gyara da muka yarda tana cikin maslaha ga ‘yan Najeriya za mu ci gaba da aiwatar da ita. Wadannan kudurorin sun kunshi tanade-tanade da ke amfanar al’umma.”
Shima a nasa jawabin, jagoran majalisar dattawan ya yi kira ga jama’a da su guji karbar labarai marasa inganci daga kafafen sada zumunta ko sauran kafafen yada labarai, ya kuma bukaci jama’a su mai da hankali ga gaskiya.