Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Umar Usman Kadafur, tare da fiye da fasinjoji 100, sun tsallake wani hatsari yayin da jirgin Max Air ya fuskanci matsala ta inji wanda ya kama da wuta jim kaÉ—an bayan ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Maiduguri.
Jaridar VANGUARD ta rawaito cewa lamarin ya faru ne kusan ƙarfe 7 na yamma a jiya Laraba, lokacin da jirgin da ke kan hanyarsa zuwa Abuja ya samu lalacewar injin sakamakon haɗari cikin mintuna 10 da tashinsa.
Daga nan ne sai matuƙin jirgin da tawagarsa su ka yi nasarar saukar gaggawa a filin jirgin saman Maiduguri, wanda hakan ne ya hana afkuwar bala'in.
Wani ma’aikacin Max Air da ya buÆ™aci a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin a safiyar yau Alhamis ga jaridar Vanguard.
Ma’aikacin ya ce: “Bayan jirgin ya tashi, ya yi karo da tsuntsu a saman iska, wanda hakan ya jawo É—ayan injin jirgin ya kama wuta. Matukin jirgin ya yi aiki cikin sauri don tabbatar da lafiyar dukkan fasinjoji.”
Bayan saukar gaggawa, an ruwaito cewa fasinjojin sun shiga halin fargaba, inda da dama daga cikinsu suka zaɓi su tattara kayansu su koma gida maimakon su shiga wani jirgin. Duk da haka, hukumar Max Air ta yi gaggawar shirya wani jirgi daga Kano don ɗaukar fasinjojin da suka ci gaba da tafiya, ciki har da Mataimakin Gwamna, lafiya zuwa Abuja.
Jirgin da ya samu matsalar dai ya tsaya a Filin Jirgin Sama na Maiduguri inda ake ci gaba da gyare-gyare. Ana ci gaba da bincike kan musabbabin lamarin.