Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPCL, ya sake duba farashin man fetur a jihohin Kano da Jigawa.
Ko da yake babban kamfanin mai na Najeriya bai fitar da sanarwa a hukumance ba kan wannan gyara, ɗaya daga cikin dillalansa da ke Kano ya shaida wa BizPoint cewa sun karɓi saƙo daren jiya don fara aiwatar da raguwar farashin.
A cewar dillalin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, an sake duba farashin lita É—aya ta man fetur a Kano zuwa N1,044 daga N1,055.
A Jigawa kuwa, farashin ya sauka zuwa N1,065 daga N1,090.
"An umurce mu da mu sake duba farashin. Daga yau, duk shagunanmu na saida man fetur za su fara siyar da farashin nan," in ji shi.