Rundunar Ƴansanda ta Jihar Kano ta yi holon wasu mutane uku da ake zargi da samun su da jabun kuɗaɗen ƙasar waje na kimanin Naira biliyan 129.
Da ya ke jawabi ga manema labarai, Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce kuɗaɗen sun haɗa da Dalar Amurka miliyan 3, 366, 000, sai kuma sefa miliyan 51, 970,000 sai kuma kudin Nijeriya Naira miliyan 1, 443.
Kiyawa ya ce ko a baya ma sun taba kama irin waɗannan masu lefin, inda ya kara da cewa rundunar ba za ta amince da irin wannan ta'ada ba.
Ya kuma baiyana gagarumin ci gaba wajen rage yawaitar aikata laifuka a fadin jihar, ta hanyar amfani da dabarun hadin gwiwa wanda ya hada da tsaron al’umma, ayyukan bincike na sirri, da kai farmaki kan maboyar masu aikata laifi.
A cewar Kwamishinan 'Yansanda, CP Salman-Dogo Garba, rundunar ta samu nasarar kama mutane 62 da ake zargi da aikata manyan laifuka, ciki har da fashi da makami, garkuwa da mutane, da kuma satar shanu, daga ranar 25 ga Nuwamba zuwa 9 ga Disamba, 2024.
CP Salman-Dogo Garba, wanda ya yi jawabi ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, a hedkwatar ‘yansanda da ke Bompai, Kano, ya bayyana cewa manyan nasarorin da aka samu sun hada da kama mutane takwas da ake zargi da fashi da makami, mutane goma da ake zargi da satar shanu, da kuma mutane uku da ake zargi da yin garkuwa da mutane.
An ceto mutum guda da aka yi garkuwa da shi da kuma wani mutum daya da aka sace, baya ga mutane 10 da aka ce suna karkashin cinikin mutane.
Kiyawa ya kuma bayyana cewa, idan akwai gaggawa ko bukatar kai rahoton wani abin da ake zargi, ana iya tuntuɓar rundunar 'yan sanda ta Kano ta wadannan lambobi: 08032419754, 08123821575, da 09029292926.
Kwamishinan ‘yan sanda ya godewa Gwamnatin Jihar Kano, sauran hukumomin tsaro, da masu ruwa da tsaki a al’umma bisa goyon baya da hadin kan da suke bai wa rundunar.