Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya tabbatar wa al'ummar karamar hukumar Bichi cewa majalisar masarauta za ta tabbatar da kai Hakimin yankin zuwa gare su cikin lumana.
Sanusi ya bayyana hakan ne yayin da wata tawagar shugabannin gargajiya da na addini karkashin jagorancin shugaban karamar hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule, suka kai masa ziyarar goyon-baya a fadar Gidan Rumfa da ke Kano a yau Laraba.
Ya ce za a sanya sabon lokaci don kai Hakimin yankin, Munir Sanusi Bayero, wanda ya yi masa nadin sarauta a kwanakin baya a fadarsa.
"Na tabbatar muku cewa za a sanya wata rana, kuma Hakimin ku za a kawo shi gare ku, kuma komai zai gudana cikin lumana," in ji shi.
A tuna cewa wannan ziyara ta zo ne kasa da mako guda bayan jami'an tsaro sun mamaye kofar shiga fadar Sarkin da zummar hana kai Hakimin yankin zuwa garin Bichi.