Shugaban kungiyar cigaban al’umma ta CDE, Amb. Ibrahim Waiya ya bukaci yan jaridun jahar Kano da su zamo masu zurfafa bincike da neman ilimi domin inganta aikin su.
Waiya ya bayyana hakan ne yayin taron karawa juna sani da kungiyar ta shiryawa yan jarida ta yadda zasu inganta aikin su a matsayinsu na wakilan A'umma .
Ya Kara dacewa akwai bukatar yan jaridu su kasance masu fadada tunani domin kaiwa mataki na kololuwa, yakuma ce an shirya bitar ne domin tunatar da manema labaran muhimmancin bin ka’idoji aikin jarida.
Wadanda suka bayar da horon ga yan jaridun sun hada da Dr. Bala Muhammad na sashin koyar da aikin Jarida na jami’ar Bayero dake nan Kano, dakuma Farfesa Nuhu Musa Idris na tsangayar shari'a dake jami'ar Bayaron .