Tsohon Sakataren gwamnatin Kano, Dakta Abdullahi Baffa Bichi ya kaiwa tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ziyara.
Ziyarar ta Bichi na zuwa ne bayan da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sauke shi daga mukamin sa a ranar Alhamis, bisa dalilin lafiya.
Babu wani labari da aka samu na takaimaimai akan abinda Sardauna Malam Ibrahim Shekarau da Dr Abdullahi Baffa Bichi suka tattauna a kai.
Saidai wasu na ganin Dr Abdullahi Baffa Bichi din zai iya komawa gidan Shekarau a PDP, yayin da wasu ke zargin zai iya komawa gidan Sanata Barau Jibiril a APC.