Majalisar Dokokin Jihar Adamawa ta amince da kudirin doka na kafa sabbin masarautu tare da nade sarakuna masu darajar ta daya a jihar.
Sabuwar dokar masarautun, wadda ke jiran amincewar Gwamna Ahmadu Fintiri, ta samu amincewa ne kwana kalilan bayan gwamnan ya rattaba hannu kan wata doka, Dokar Kirkiro Gundumomi ta Jihar Adamawa 2024, wadda ta samar da sabbin gundumomi guda 83 a ranar 4 ga Disamba.
A wata wasika da Mr. Fintiri ya aikewa 'yan majalisar a ranar Litinin, ya bukaci su amince da kudirin doka da zai bayar da damar nade sarakuna da cire su daga mukamansu a jihar Adamawa.
Kudirin ya bai wa gwamnan ikon kafa karin masarautu tare da nada ko tsige shugabannin gargajiya.
Kudirin dokar ya tsallake karatun farko da na biyu a Majalisar Dokokin Jihar a ranar Litinin.
Dokar ta rage tasirin Lamidon Adamawa, Alhaji Muhammadu Barkindo, ta hanyar takaita yawan kananan hukumomin da ke karkashinsa daga takwas zuwa uku.