Hon Isah yace, zaiyi aiki kafa da kafa da shugaban karamar hukuma dama wakilan yankinsu na Tarayya da jaha domin gannin karamar hukumar kura tarike kambon karamar hukumar datafi kowacce karamar hukuma a fannin kiwon lafiya.
Babu wani shugaba daya tafiyar da al'umma akayi aiki cikin nasara dole sai da hadin kan al'ummar da kake mulka, a don haka ina kira da Al'ummar karamar hukuma ta da subamu goyon baya dari bisa dari domin ceto yankin daga halin data tsinci kanta a gwamnatin data shude,
Gwamnatinmu kofofinta a bude suke tunda Gwamnatin Jiha karkashin jagorancin Mai Girma Gwamna Alh. Abba Kabir Yusuf da Dan majalisar mu na wakilan Tarayya da Dan majalisar mu na jiha da shugaban karamar hukuma dama dukkan ninmu masu taimaka masa duk wanda yake da shawara wajen bunkasar karamar hukumar Kura muna marhabin da shi. Inji shi