Shugaban karamar hukumar Gwale dake jihar Kano, Hon Abubakar Mu'azu Mojo, yace a shirye yake ya sauka daga kan Kujerarsa matukar dai ba'a canja masa Daraktan mulki na karamar hukumar ba.
Mojo ya zargi Daraktan mulkin, Danjuma Zubairu Bebeji, da kawo cikas a manufofin Gwamnatin jihar Kano na kyautatawa al'umma, domin kuwa takardun al'umma suna bata a Ofishinsa ba tare da wani cikakken dalili ba, saboda haka ya rubuta takarda zuwa ma'aikatar kananan hukumomin jihar domin ta kawo masa wani Daraktan.
Bugu da kari, Mojo yace tun lokacin da yana Kantoman Gwale yake samun matsala daga Daraktan mulkin, amma ya yafe masa, sai dai har yanzu bai canja hali ba, "ni kuma na nemi shugaban karamar hukuma ne domin na taimaki Mutane, zanyi aiki da kowanne ma'aikacin Gwamnati da yake da burin taimakon al'umma, musamman al'ummar karamar hukumar Gwale." - a cewar Mojo