Dole a gaggauta sulhunta Kwankwaso da Ganduje ~ Abdulmuminu Kofa
Shugaban kwamitin gidaje da muhalli na Majalisar Wakilai, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya yi kira da a gaggauta sulhunta tsakanin tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje.
Kofa ya bayyana haka ne a wata hira da gidan rediyo a Kano a jiya Alhamis, inda ya bayyana takaddamar da ke tsakanin manyan jiga-jigan siyasar biyu a matsayin abin takaici da kuma illa ga jihar.
Ya kuma bukaci manya masu kishin Kano da su hada hannu wajen sulhunta jagororin siyasar biyu domin ci gaban jihar.
Da ya ke bayyana nasarorin da su biyun su ka samu, Jibrin ya bayyana cewa shugabannin biyu sun yi fice a aikin gwamnati da kuma samar wa Kano aiyukan more rayuwa.
Ya danganta yawancin kalubalen siyasar Kano da tsamin dangantakar da ke tsakanin shugabannin biyu, ya na mai kira ga magoya bayansu da su baiwa zaman lafiya fifiko.