Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta amince da kudirin gyaran dokar haraji, inda ta ba da shawarar cewa kada a kara harajin VAT kuma ta gabatar da muhimman shawarwari.
”Kungiyar ta amince da sabon tsarin raba kuÉ—in harajin (VAT) domin tabbatar da daidaiton rarraba arzikin kasa kamar haka :
Kashi 50% bisa daidaito,
30% bisa la’akari da abin da aka samar,
20% bisa yawan jama’a.
”Mambobin sun amince cewa bai kamata a kara harajin VAT ba ko rage Harajin KuÉ—in Shiga na Kamfanoni (CIT) a wannan lokaci, don kiyaye daidaiton tattalin arziki. Kungiyar ta nemi a ci gaba da ware kayan masarufi da kayan noma daga harajin VAT don kare walwalar 'yan Æ™asa da Æ™arfafa aikin gona.
”Taron ya bayar da shawarar cewa bai kamata a saka sharadin rushe hukumomi irin su TETFUND, NASENI, da NITDA kamar yadda ya ke a kudirin dokar”.