Hukumar tace fina-finai ta haramtawa Usman Sojaboy da wasu mata biyu shiga harkokin Film ko waka a jahar Kano.
Hukumar tace fina-finai da Dab'i ta Jahar Kano ta bayyana matsayarta kan korafe-korafen da al'umma suka shigar gabanta, tare da wasu malamai a Jahar, kan Usman wanda akafi sanni da Sojaboy, dangane da wani sabon salon waka da yake kokarin fitowa da shi, wanda ya saba da koyarwar addinin musulunci tare da al'adar malam Bahaushe.
A wata sanarwa da jami'in yada labaran Hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar, ya bayyana cewa Shugaban Hukumar Abba El-mustapha ya amince da kwace lasisin mawakin Sojaboy da Shamsiyya Muhammad tare da Hassana Suzan, ya yin da sanarwa ta bukaci masu gidajen wasanni tare duk wani wannda yake mu'amalar aiki dasu da ya yi biyayya ga wannan matakin na Hukumar domin cigaban Jahar Kano.
Abba El-mustapha ya baiwa sashin tace fina-finai na Hukumar umarnin cewa, daga wannan lokacin kada a Kara tace duk wani film da aka hangi fuskokinsu a ciki, tare da kira ga masu shirya fina-finai musamman daraktoci da su kiyayi yin duk wata huldar aiki dasu domin gujewa fishin Hukumar.
Kafin ta dauki irin wannan matakin Hukumar na yin iya kokarinta kan gargadar masu irin wannan halayya, dasu kiyayi yin duk wani abu da zai zubar da kimarsu ko Sana'arsu, inda ta kara jaddada cewa buzata dauki duk wani abu da zai taba addini, al'ada ko tarbiyar a'lummar Jahar Kano da sauki ba.
Haka kuma, bazata goyi bayan ire-iren wannan halayyar ba da sunan sana'a a Jahar Kano.
Idan ba'a manta ba a watan da ya gabata ne Hukumar ta dauki irin wannan mataki ga daya daga cikin fitattun jarumai a Masana'antar ta kannywood, wato Samha M Inuwa da nufin tsaftace Masana'antar tare da tabbatar da kowa nabin dokokin Hukumar sau da kafa.