Kotun Ma'aikata a Jihar Kano ta shawarci Gwamnatin Jihar da su hau teburin sulhu tsakanin su da tsaffin kansiloli
Kotun ma'aikata a Kano ta baiwa Gwamnatin Kano shawara da su hau teburin sulhu da tsofaffin kansiloli da mataimakan shugaban kananan hukumomi da sakatarori kan hakkokin su da ba a biya su ba a shekarun baya, da suka hada da zaɓaɓɓu da naɗaɗɗu daga shekara ta 2018 zuwa ta 2021 da 2024.
Lauyan da ke tsaya musu Barista Abba Hikkima Fagge, ya nemi da a bada wata rana domin kara shigo da wasu cikin shari'ar duba da yawan mutanen da suke ciki, yace a shirye suke idan Gwamnatin ta nemi su zauna domin sulhuntawar.
A nasa bangaren Lauyan dake wakiltar Kananan Hukumomi Barista Bashir Tudun Wuzirci, wanda Barista Umar Bala Salisu yace suna wakltar kananan hukumomi ne kuma a shirye suke da su zauna da masu kara domin yin sulhu.
Justice M.A NAMTARI ya dage cigaba da shari'ar zuwa ranar 12 ga watan Maris din wannan shekarar domin bude ƙofar yin sulhun.
Guda daga cikin jagororin tafiyar tsohon mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Dala, Sagir Sani Ahmad, yace abin maraba ne idan Gwamnatin ta nemi da ayi Sulhun.