Kwamishinan na wannan kirane a lokacin daya shiga ofishinsa, inda yace yayi alkawarin zaiyi aiki tukuru wajen ciyar da Jihar Kano gaba.
Comr Waiya yace hukumar sa zatayi aiki babu kama hannun yaro, musamman wajen kare muradan gwamnati jihar kano karkashin jagorancin Gwamna Alh. Abba Kabir Yusuf.
Yayi alkawarin farfadu da dukkanin jami'an watsa labarai na hukumomin Jihar Kano domin bayyana ayyukansu cikin kwarewa da sannin yakamata.
Taron yasamu halattar Yan jaridu daga kafafen watsa labarai na Jihar kano da shugabannin ma'aikatun jarida da shugaban jam'iyyar NNPP na karamar hukumar Dala Alh. Dayyabu Maiturare, da masu taimakawa Gwamna a bangaren watsa labarai da dai sauransu
Kafin bashi Kwamishinan watsa labarai Waiya yayi aiki daban-daban wajen kare hakkin Dan Adam dama sauran kungiyoyi na kwato hakkin wanda aka zalunta, da kungiyoyin jagorantar zaman lafiya a kasa dama wasu sassan kasarnan da dama.