A madadin Shugabancin gidan Talabijin na ARTV karkashin jagorancin shugabar gidan Hajiya Hauwa Isa Ibrahim, da maitamaka mata Hon Idris Musa Abba, dama daukacin ma'aikatantana na mika sakon taya sabon Kwamishinan yada labarai, Comr Ibrahim A. Waiya murnar karbar rantsuwa a yau.
Tana mai addu'ar Allah shi rika, yabasu ikon sauke nauyin da Maigirma Gwamna Alh. Abba Kabir Yusuf ya dora musu wajen ciyar da Jihar Kano gaba
Allah ya taya riko 🙏
Wannan na kunshine a wata sanarwa ta bakin Babban mataimaki na musamman ga shugabar Gidan Talabijin na ARTV, Jameel Lawan Yakasai a wannan rana ta litinin 06-01-2025, daya wallafa a shafinsa na kafar Facebook.